Ezekiel 1:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk inda ruhu za shi, su ma can za su, kuma da’irorin za su tashi tare da su, domin ruhun rayayyun halittun nan yana a cikin da’irorin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ عِنْدَ رُوحٌ يَمُواْڟَسُ، حَلِتُّنَّنْ سُكَنْبِے، ڧَڢَاڢُنَّنْ سُو مَا سُكَنْ تَڢِے تَرٜىٰدَسُو؞ غَمَا رُوحٌ حَلِتُّنْ يَنَ ثِكِنْ ڧَڢَاڢُنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Duk inda ruhu ya nufa, sai talikan su bi, sai kuma ƙafafun su tafi tare da su, gama ruhun talikan yana cikin ƙafafun.