Ezekiel 1:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da halittun sun motsa, sai su ma su motsa; sa’ad da halittun sun tsaya cik, su ma sai su tsaya cik, sa’ad da kuma halittun sukan tashi sama, da’irorin suka tashi tare da su, domin ruhun rayayyun halittun nan yana a cikin da’irorin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ سَعَدَّ حَلِتُّنْ سُكَ مُواْڟَ، ڧَڢَاڢُنْ مَا سُكَنْ مُواْڟَ؞ دُكْ سَعَدَّ حَلِتُّنْ سُكَ ڟَيَ، ڧَڢَاڢُنْ مَا سُكَنْ ڟَيَ؞ دُكْ سَعَدَّ حَلِتُّنْ سُكَتَاشِ سَمَ، ڧَڢَاڢُنْ مَا سُكَنْ تَاشِ سَمَ تَرٜىٰدَسُو؞ غَمَا رُوحٌ حَلِتُّنْ يَنَ ثِكِنْ ڧَڢَاڢُنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan talikan sun motsa, sai ƙafafun kuma su motsa. Idan sun tsaya cik, sai su ma su tsaya. Idan kuma talikan sun ɗaga sama, sai ƙafafun su ɗaga sama tare da su, gama ruhun talikan yana cikin ƙafafun.