Ezekiel 1:26 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A bisa al’arshin a kan kawunansu akwai abin da ya yi kamar saffaya, kuma a can bisa a kan kursiyin akwai siffa kamar na mutum.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَبِسَنْ مُرْڢِنْ دَيَكٜىٰ سَمَ دَ كَنْ حَلِتُّنْ، أَݣَويْ وَنِ أَبُ كَمَرْ كُجٜىٰرَرْ مُلْكِ، وَدَّ عَكَيِ دَ دُوڟٜىٰنَّنْ سَڢَّيَ مَيْ دَرَجَ؞ عَثَنْ بِسَ أَݣَويْ وَنِ مَيْ كَمَنِّنْ مُتُمْ يَنَ ظَوْنٜىٰ عَكَنْ أَبِنْدَ يَكٜىٰ كَمَرْ كُجٜىٰرَرْ مُلْكٍ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A saman al'arshin akwai wani abu mai kamar kursiyin sarauta da aka yi da yakutu. Akwai wani kamar mutum yana zaune a kan abin nan mai kama da kursiyin sarauta.