Ezekiel 10:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yayinda suke tafiya, sukan tafi kowane gefe huɗun da kerubobin suka nufa; da’irorin ba sa juyawa yayinda kerubobin suke tafiya. Kerubobin suka tafi kowane gefen da kan ya nufa, ba tare da juyawa ba sa’ad da suke tafiya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ ذَاسُيِ غَبَ، أَدُكْ غٜىٰڢٜىٰ طَيَ عَثِكِنْ ݣُونَ حُطُنْ دَ سُكَ نُڢَ، ذَاسُيِ تَڢِيَ تَرٜىٰ، كُمَ بَاتَرٜىٰدَ جُويَا جِكِنْسُبَ؞ عَمَّا دُكْ عِنْدَ ڧَڢَرْ غَبَ تَنُڢَ، دُكَنْ سَوْرَنْ ذَاسُبِے، بَ سَيْ سُنْ جُويَا بَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da suke tafiya, sukan tafi kowane waje, ba sai sun juya ba. Duk wajen da ƙafar gaba ta nufa, nan sauran za su bi, ba sai sun juya ba.