Ezekiel 10:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yayinda nake duba, kerubobin suka buɗe fikafikansu suka kuma tashi daga ƙasa, yayinda suka tafi kuwa, da’irorin suka tafi tare da su. Suka tsaya a mashigin ƙofar gabas na gidan Ubangiji, ɗaukakar Allah na Isra’ila kuwa yana a kansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ عِدُواْنَ، سَعَدَّ حَلِتُّو مَاسُ ڢِكَڢِكَيْ سُكَ ڢِتَ، سُكَتَادَ ڢِكَڢِكَنْسُ سُكَتَاشِ سَمَ دَغَ ڧَسَا، ڧَڢَاڢُنْ سُنَانَنْ عَكُواْوَنٜىٰ غٜىٰڢٜىٰنْسُ؞ سُكَ ڟَيَ عَڧُواْڢَرْ غَبَسْ نَغِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ ڧُنْشِنْ حَصْكٜىٰنْ طَوْكَكَرْ اللَّهْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ يَنَ بِسَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kerubobin kuwa suka ɗaga fikafikansu, suka tashi daga ƙasa, suka yi sama a kan idona, suka tafi da ƙafafun gab da su. Suka tsaya a ƙofar gabas ta Haikalin Ubangiji. Ɗaukakar Allah na Isra'ila kuwa tana bisa kansu.