Ezekiel 11:16 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Saboda haka ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ko da yake na kore su zuwa cikin al’ummai na kuma warwatsa su cikin ƙasashe, duk da haka na zama wuri mai tsarki a gare su a ƙasashen da suka tafi.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ، سَيْ كَثٜىٰ مُسُ إِنْجِنِ عُبَنْ‌غِجِ يَهْوٜىٰهْ ، ‹كُواْدَيَكٜىٰ نَكَيْسُ دَ نٜىٰسَ ثِكِنْ أَلْعُمَّيْ، نَاكُوَ وَاڟَرْ دَسُو عَثِكِنْ ڧَسَاشٜىٰ، دُكْدَهَكَ أَغَرٜىٰسُ نَذَمَ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے نَطَنْ لُواْكَثِ عَثِكِنْ ڧَسَاشٜىٰنْ دَ عَكَ كَيْسُ؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Domin haka, ka ce, ‘Ni Ubangiji Allah na ce, ko da yake na kai su nesa tsakanin al'ummai, na warwatsa su cikin ƙasashe, duk da haka na zama Haikali a gare su a ɗan lokaci, a ƙasashen da suka tafi.’