Ezekiel 12:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ka faɗa wa mutanen ƙasar cewa, ‘Ga abin Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa game da waɗanda suke zama a Urushalima da kuma cikin ƙasar Isra’ila. Za su ci abincinsu da razana, su sha ruwansu da tsoro, gama za a washe dukan abin da yake ƙasarsu saboda hargitsin dukan waɗanda suna zama a can.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَثٜىٰ وَمُتَنٜىٰنْ ڧَسَرْ، ‹إِنْجِنِ عُبَنْغِجِ يَهْوٜىٰهْ غَمٜىٰدَ مَذَوْنَنْ عُرُوشَلِيمَ وَطَنْدَ سُكٜىٰ عَثِكِنْ ڧَسَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ ذَاسُثِ عَبِنْثِنْسُ دَ ضَوَرْ جِكِے، سُكُمَ شَا ضُوَنْسُ دَ ڟُواْرُواْ، غَمَا ذَاعَ ݣُوشٜىٰ دُكَنْ أَبِنْدَ يَكٜىٰ ثِكِنْ ڧَسَرْسُ، سَبُواْدَ تَاشِنْ حَنْكَلِنْ دُكَنْ وَطَنْدَ سُكٜىٰ ظَوْنٜىٰ عَثِكِنْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ka faɗa wa mutanen ƙasar, cewa ni Ubangiji Allah na ce mutanen Urushalima da suke a ƙasar Isra'ila za su ci abincinsu da razana, su sha ruwansu da tsoro, gama za a washe dukan abin da yake ƙasarsu saboda hargitsin dukan waɗanda suke zaune cikinta.