Ezekiel 12:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma Ni Ubangiji zan yi magana abin da na nufa, za tă kuwa tabbata ba tare da jinkiri ba. Gama cikin kwanakinku, kai gidan ’yan tawaye, zan cika duk abin da na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا نِے يَهْوٜىٰهْ ذَنْيِ مَغَنَ، مَغَنَرْ دَ ذَنْ ڢَطَا كُوَ ذَاعَ ثِكَتَ؞ بَذَاتَ سَاكٜىٰ دَطٜىٰوَبَ، عَمَّا عَثِكِنْ ݣُونَكِنْكُ، يَا كُو جَمَعَتَ مَاسُ تَاوَيٜىٰ، ذَنْيِ مَغَنَ إِنْكُمَ ثِكَتَ؞ نِے عُبَنْ‌غِجِ يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama ni Ubangiji zan yi magana, maganata kuwa za ta tabbata, ba za ta yi jinkiri ba, amma za ta tabbata a kwanakinku, ku 'yan tawaye. Zan yi magana, za ta kuwa tabbata, ni Ubangiji Allah, na faɗa.”