Ezekiel 13:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Domin sun ɓad da mutanena, suna cewa, “Salama,” sa’ad da ba salama, kuma saboda, sa’ad da ana gina katanga marar ƙarfi, sukan shafe ta da farar ƙasa,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَنْيِ حَكَ، غَمَا سُنْ رُوطِ مُتَنٜىٰنَ سُنَ ثٜىٰوَ ‹سَلَمَ،› سَعَدَّ بَابُ سَلَمَ؞ سَعَدَّ عَكَ غِنَا كَتَنْغَ مَرَرْ ڧَرْڢِے، سَيْ أَنَّبَاوَنْ سُشَاڢَ دَ ڢَرَرْ ڧَسَا دُواْمِنْ عَڧَارَ مَتَ ڧَرْڢِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Domin sun ɓad da mutanena suna cewa, ‘Salama,’ sa'ad da ba salama, sa'ad da kuma mutanen suke gina garu marar aminci, sai annabawan nan su shafe shi da farar ƙasa,