Ezekiel 13:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
saboda haka ka faɗa wa waɗanda suka shafe da farar ƙasa cewa za tă fāɗi. Ruwan sama zai sauko da rigyawa, zan kuma aika da ƙanƙara, kuma babbar iska za tă ɓarke.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ كَڢَطَا وَ وَطَنْدَ سُكَ شَاڢٜىٰ كَتَنْ‌غَرْ دَ ڢَرَرْ ڧَسَا ثٜىٰوَ ذَاتَڢَاطِ؞ ذَاعَيِ ضُوً سَمَ دَ ڧَنْڧَرَ دَ إِسْكَ مَيْ ڧَرْڢِے وَنْدَ ذَيْ رُشٜىٰتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ka faɗa wa waɗanda suka shafe garun da farar ƙasa, cewa zai faɗi. Za a yi rigyawa da ƙanƙara, da babban hadiri mai iska.