Ezekiel 13:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kun jawo mini kunya a cikin mutanena don a tafa muku sha’ir da ɗan dunƙulen burodi. Ta wurin yin ƙarya wa mutanena, waɗanda suke jin ƙarairayi, kuka kashe waɗanda bai kamata su mutu ba kuka bar waɗanda ya kamata su mutu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاكُيِ بَنْظَ دَ سُونَنَ عَثِكِنْ مُتَنٜىٰنَ دُواْمِنْ كُسَامِ حَڟِنْ بَلٜىٰ كَطَنْ عَتَڢِنْ حَنُّوَنْكُ، كُسَامِ طَنْ غُرَاسَ كَطَنْ؟ تَوُرِنْ ڧَضْيَارْكُ، غَ مُتَنٜىٰنَ وَطَنْدَ سُكَ كَسَ كُنّٜىٰ غَ ڧَضْيَاثٜىٰ ڧَضْيَاثٜىٰنْكُ، كُنَ كَشٜىٰ مُتَنٜىٰنْ دَ بَيْ كَمَاتَ سُمُتُبَ، كُنَ بَرِنْ وَطَنْدَ بَيْ كَمَاتَ سُرَايُبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kun saɓi sunana a cikin mutanena don a tafa muku sha'ir, a ba ku ɗan abinci. Kuna kashe mutane waɗanda bai kamata su mutu ba, kuna barin waɗanda bai kamata su rayu ba ta wurin ƙaryace-karyacen da kuke yi wa mutanena waɗanda suke kasa kunne ga ƙaryace-ƙaryacen.’