Ezekiel 13:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
saboda haka ba za ku ƙara ganin wahayin ƙarya ba, ko ku yi duba. Zan ceci mutanena daga hannuwanku. A sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
حَڧِيڧَ بَذَاكُ ڧَارَ غَنِنْ رُعُيَرْكُ تَڧَضْيَا كُواْ كُيِ دُوبَانْ ڧَضْيَابَ؞ ذَنْ كُٻُتَرْدَ مُتَنٜىٰنَ دَغَ حَنُّنْكُ؞ سَعَنً ذَاكُ سَنِ ثٜىٰوَ نِنٜىٰ يَهْوٜىٰهْ ؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Domin haka ba za ku ƙara ganin wahayin ƙarya ba, ko ku yi dūba. Zan ceci mutanena daga hannunku. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji.”