Ezekiel 14:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan mutanen Isra’ila ba za su ƙara kauce daga gare ni ba, ba kuwa za su ƙara ƙazantar da kansu da dukan zunubansu ba. Za su zama mutanena, ni kuma zan zama Allahnsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَنْيِ حَكَ دُواْمِنْ كَدَ غِدَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُڧَارَ كَوْثٜىٰوَ دَغَ غَرٜىٰنِ، كُواْ سُڧَارَ ڧَظَنْتَرْ دَكَنْسُ دَ ذُنُبَنْ غَنْ‌غَنْثِنْسُ؞ ذَاسُ ذَمَ مُتَنٜىٰنَ، نِے كُمَ إِنْذَمَ اللَّهْ نْسُ؞ نِے عُبَنْ‌غِجِ يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
don kada mutanen Isra'ila su ƙara rabuwa da ni, ko kuma su ƙara ƙazantar da kansu ta wurin laifofinsu, amma za su zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnsu,’ ni Ubangiji Allah na faɗa.”