Ezekiel 14:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka ka yi musu magana ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa sa’ad da wani mutumin Isra’ila ya kafa gumaka a cikin zuciyarsa ya kuma sa mugun abin tuntuɓe a gabansa sa’an nan ya tafi wurin annabi, Ni Ubangiji zan amsa masa da kaina game da babban bautar gumakarsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ، كَڢَطَا مُسُ ثٜىٰوَ ‹إِنْجِنِ عُبَنْغِجِ يَهْوٜىٰهْ ، دُكْ مُتُمِنْ غِدَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ وَنْدَ يَكَڢَ ذُوثِيَارْسَ عَكَنْ غُمَكَ، يَكُمَسَا مُغُنْتَا تَذَمَ أَبِنْ تُنْتُٻٜىٰ أَغَبَنْسَ، سَعَنً يَذُواْ وُرِنْ أَنَّبِے، نِے يَهْوٜىٰهْ دَكَيْنَ ذَنْبَاشِ أَمْسَ بِسَغَ يَوَنْ غُمَكَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Sai ka faɗa musu, cewa Ubangiji Allah ya ce duk mutumin Isra'ila, wanda ya manne wa gumaka, ya sa abin tuntuɓe a gabansa sa'an nan kuma ya zo wurin annabi, ni Ubangiji zan sāka masa gwargwadon yawan gumakansa,