Ezekiel 16:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Haka kuwa aka caɓa miki zinariya da azurfa; tufafinki kuwa na lilin mai kyau da riguna masu tsada waɗanda aka yi musu ado. Abincinki na gari mai laushi ne, zuma da man zaitun. Kika zama kyakkyawa har kika kuma zama sarauniya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تَهَكَ أَنْيِ مِكِ أَدُواْ دَ ظِينَارِيَ دَ أَظُرْڢَا؞ رِيغُنَنْكِ كُوَ نَلِيلِنْ نٜىٰ مَيْݣَوْ دَ ذَنُّوَ مَاسُ ڟَادَ مَاسُ أَدُوانْ سَاڧَ؞ كِنْ ثِ عَبِنْثِ مَڢِے ݣَوْ دَ ظُمَ دَ مَيْ؞ كِنْ ذَمَ ݣَكْݣَاوَا ڨُورَيْ دَ غَسْكٜىٰ، كِنْ يِغِرْمَ حَرْ كِنْ كَيْ دَرَجَرْ سَرَوْنِيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Haka kuwa aka caɓa miki zinariya da azurfa. Tufafinki kuwa na lilin mai kyau ne, da siliki waɗanda aka yi musu ado. Kin ci lallausan gāri, da zuma, da mai. Kin yi kyau ƙwarai har kin zama sarauniya.