Ezekiel 16:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Cikin dukan ayyukan banƙyamarki da karuwancinki ba ki tuna da kwanakin ƙuruciyarki ba, sa’ad da kike tsirara tik, kina birgima cikin jininki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَثِكِنْ دُكَنْ أَبُبُوَنْكِ نَڧَظَنْتَادَ كَارُوَنْثِنْكِ، بَاكِ تُنَ دَ ݣُونَكِنْ ڧُرُثِيَرْكِ بَ، لُواْكَثِنْ دَ كِكٜىٰ ڟِرَرَ بَابُ رِغَا، كِنَ بِرْغِمَ عَثِكِنْ جِنِنْ حَيْڢُوَرْكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A cikin aikata dukan abubuwanki na banƙyama kuma, da karuwancinki, ba ki tuna da kwanakin kuruciyarki ba, lokacin da kike tsirara tik, kina birgima cikin jinin haihuwarki.