Ezekiel 16:31 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da kika gina ɗakunan samanki a kowane gefen titi kika kuma gina ɗakunan tsafinki a kowane dandali, ba kamar karuwa kike ba, domin kin karɓi kuɗi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كِنْيِ حَصُومِيَا عَكُواْوَثٜىٰ ݣُونَ تَتِيتِ، كِنْ كُمَ غِنَا وُرِنْ سُجَّدَ عَكُواْوَنٜىٰ ڢِيلِ نَثِكِنْ غَرِ! دُكْدَهَكَ، كٜىٰ بَاكِ نُونَ حَلِنْ كَارُوَبَ دَيَكٜىٰ بَاكِ كَرْٻِ كُطِبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kin gina ɗakunan tsafi a kowane titi da kowane fili. Amma ke ba kamar karuwa ba ce, da yake ba ki karɓar kuɗi.