Ezekiel 16:45 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ke ’yar mahaifiyarki ce da gaske, wadda ta ƙi mijinta da ’ya’yanta; ke kuma ’yar’uwar ’yar’uwanki mata ce da gaske, waɗanda suka ƙi mazansu da ’ya’yansu. Mahaifiyarki mutuniyar Hitti ce, mahaifinki kuma mutumin Amoriyawa ne.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كٜىٰثٜىٰ یَرْ مَامَرْكِ وَدَّ تَڧِے مِجِنْتَ دَ یَیَنْتَ؞ كٜىٰثٜىٰ یَرْعُوَرْ یَنْعُوَنْكِ مَتَ وَطَنْدَ سُكَڧِ مَذَنْسُ دَ یَیَنْسُ؞ حَڧِيڧَ، مَامَرْكِ مَثٜىٰثٜىٰ دَغَ هِتِّ، بَابَنْكِ مُتُمِنْ أَمُواْرِيَاوَا نٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ke 'yar mahaifiyarki ce wadda ta ƙi mijinta da 'ya'yanta. Ke kuma 'yar'uwar 'yar'uwanki mata ce waɗanda suka ƙi mazansu da 'ya'yansu. Mahaifiyarki Bahittiya ce, mahaifinki kuwa Ba'amore ne.