Ezekiel 16:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba wanda ya dube ki da tausayi ko ya nuna miki isashen jinƙai don yă yi miki ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa. A maimako, sai aka jefar da ke a fili, gama a ranar da aka haife ki an ji ƙyamarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَاوَنْدَ يَجِ تَوْسَيِنْكِ دَ ذَيْ يِمِكِ وَطَنَّنْ أَبُبُوَ نَجِنْڧَيْ؞ عَمَّا عَكَ جٜىٰڢَرْ دَكٜىٰ أَدَاجِ، غَمَا كِنْ ذَمَ أَبِنْ ڨَمَ أَ رَانَرْ دَ عَكَ حَيْڢٜىٰكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba wanda ya ji tausayinki da zai yi miki waɗannan abubuwa na jinƙai, amma aka jefar da ke a waje, gama kin zama abin ƙyama a ranar da aka haife ki.