Ezekiel 16:52 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ki sha kunyarki, gama kin yi rangwame wa ’yan’uwanki mata. Saboda zunubanki sun yi muni fiye da nasu, sai suka zama kamar sun fi ki adalci. Saboda haka, ki sha kunya ki kuma sha ƙasƙancinki, gama kin sa ’yan’uwanki mata suka zama kamar su masu adalci ne.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كٜىٰ كُوَ سَيْ كِطَوْكِ كُنْيَرْكِ! غَمَا كِنْسَا یَنْعُوَنْكِ مَتَ سُسَامِ حُكُنْثِ مَيْ سَوْڧِ سَبُواْدَ ذُنُوبِنْ دَ كِكَ عَيْكَتَ يَڢِنَاسُ بَنْ ڨَمَ؞ سُنْڢِيكِ أَدَلْثِے؞ عِ، كِشَا كُنْيَرْكِ، كِشَا ڧَسْڧَنْثِنْكِ، غَمَا كِنْسَا یَنْعُوَنْكِ مَتَ سُنْذَمَ كَمَرْ مَاسُ أَدَلْثِے؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ke kuma sai ki sha kunyarki, gama kin sa 'yan'uwanki mata su sami rangwamin shari'a saboda zunubanki da kika aikata fiye da nasu, gama gwamma su da ke. Sai ki ji kunya, ki sha ƙasƙancinki, gama kin sa 'yan'uwanki mata su zama kamar adalai.”