Ezekiel 17:23 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A ƙwanƙolin dutsen Isra’ila zan shuka shi; zai yi rassa yă ba da ’ya’ya yă kuma zama al’ul mai daraja. Tsuntsaye iri-iri za su yi sheƙa a cikinsa; za su sami mafaka a inuwar rassansa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَكَنْ بَبَّنْ تُدُنْ إِسْرَٰٓءِيلَ ذَنْ دَسَ شِ، دُواْمِنْ يَڢِتَرْدَ رَسَّ دَيَوَ، يَبَادَ یَیَ، يَذَمَ إِتَاثٜىٰنْ سٜىٰدَ نَڨُورَيْ؞ ڟُنْڟَيٜىٰ إِرِ إِرِ ذَاسُذُواْ سُذَوْنَ عَڧَرْڧَشِنْسَ، ذَاسُيِ غِدَاجٜىٰنْسُ عَثِكِنْ إِنُوَرْ رَسَّنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A ƙwanƙolin tsaunin Isra'ila zan dasa shi Don ya fito da rassa, ya ba da 'ya'ya, Ya zama itacen al'ul na gaske. Tsuntsaye iri iri za su zauna a ƙarƙashinsa, Za su yi sheƙuna a cikin inuwar rassansa.