Ezekiel 17:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Akwai kuma wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai da gashi mai yawa. Kuringan nan ta tanƙwasa saiwoyinta zuwa wajen wannan gaggafa daga inda aka shuka ta, ta kuma miƙe rassanta wajenta don gaggafar ta yi mata banruwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
« ‹عَمَّا أَݣَويْ كُمَ وَتَ بَبَّرْ غَغَّڢَ دَبَمْ مَيْ مَنْيَنْ ڢِكَڢِكَيْ دَ غَاشِ مَيْ يَوَ؞ غَاشِ، إِتَاثٜىٰنْ إِنَبِنَّنْ يَجُويَ سَيْوُاْيِنْسَ يَمِيڧَ رَسَّنْ ذُوَا وُرِنْ غَغَّڢَرْ نَنْ، دُواْمِنْ عِتَ تَيِ مَسَ بَنْ ضُوَ أَمَيْمَكُوانْ ڧَسَا عِنْدَ عَكَ شُوكَشِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“ ‘Akwai kuma wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai da gashi mai yawa. Sai wannan kuranga ta tanƙwasa saiwoyinta zuwa wajenta, ta kuma miƙe rassanta zuwa wajenta tun daga inda aka dasa ta, don gaggafar ta yi mata banruwa.