Ezekiel 17:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ka gaya musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wannan za tă ci gaba? Ba za a tumɓuke ta a kuma kakkaɓe ’ya’yanta don ta bushe ba? Dukan sababbin tohonta za su bushe. Ba sai da hannu mai ƙarfi, ko kuwa da yawan mutane za a tumɓuke ta daga saiwoyinta ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«سَيْ كَثٜىٰ وَجَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ، ‹إِنْجِنِ عُبَنْغِجِ يَهْوٜىٰهْ ، إِتَاثٜىٰنْ إِنَبِنَّنْ ذَيْ رَايُ كُوَ؟ أَشٜىٰ، بَغَغَّڢَ تَڢَرْكُواْ ذَاتَ تُمْٻُكٜىٰ سَيْوُاْيِنْسَ تَكُمَ كَكَّٻٜىٰ یَیَنْسَ دُواْمِنْ دُكَنْ غَنْيَيٜىٰنْسَ سُبُوشٜىٰبَ؟ أَيْ، بَسَيْ دَ حَنُّ مَيْ ڧَرْڢِے، كُواْ دَ مُتَنٜىٰ دَيَوَ ذَاعَ تُمْٻُكٜىٰشِ دَغَ سَيْوُاْيِنْسَبَ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Ko wannan kurangar inabi za ta ci gaba? Ashe, gaggafa ta farko ba za ta tumɓuke saiwoyinta, ta sassare rassanta, don ganyayenta da suke tohuwa su bushe ba? Ba sai da hannu mai ƙarfi, ko kuwa da yawan mutane za a tumɓuke ta daga saiwoyinta ba.