Ezekiel 18:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai sami rabo a laifin mahaifi ba, mahaifi ba zai sami rabo a laifi ɗa ba. Adalcin adali zai zama nasa, muguntar mugu za tă koma kansa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ مُتُمِنْ دَ يَيِ ذُنُوبِ، شِ ذَيْ مُتُ؞ طَا بَذَيْ طَوْكِ أَلْحَكِنْ لَيْڢِنْ بَابَنْسَبَ، حَكَمَا بَابَ بَذَيْ طَوْكِ أَلْحَكِنْ لَيْڢِنْ طَنْسَبَ؞ يِنْ أَدَلْثِے نَمَيْ أَدَلْثِے ذَيْ كَسَنْثٜىٰ عَكَنْسَ، يِنْ مُغُنْتَا نَمُوغُ كُمَ ذَيْ كَسَنْثٜىٰ عَكَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wanda ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai ɗauki hakkin laifin mahaifinsa ba, mahaifi kuma ba zai ɗauki hakkin laifin ɗansa ba. Adalcin adali nasa ne, muguntar mugu kuma tasa ce.