Ezekiel 18:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Amma in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya yi zunubi ya kuma aikata abubuwa masu banƙyamar da mugun mutum ke aikatawa, zai rayu? Babu abubuwan adalcin da ya aikata da za a tuna da su. Saboda rashin amincinsa da kuma saboda zunubai da ya yi, zai mutu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«عَمَّا عِدَنْ مَيْ أَدَلْثِے يَجُويَ دَغَ يِنْ أَدَلْثِے، يَعَيْكَتَ ذُنُوبِ دَ أَبُبُوَنْ بَنْ ڨَمَ وَطَنْدَ مُوغُ يَكٜىٰ عَيْكَتَاوَا، أَغَنِنْكُ ذَيْ رَايُ؟ أَيْ، بَذَاعَ تُنَ دَ أَيُّكَنْسَ نَأَدَلْثِے وَطَنْدَ دَا يَكٜىٰيِبَ! سَبُواْدَ رَشِنْ أَمِنْثِنْ دَ يَيِ دَ ذُنُوبِنْدَ يَعَيْكَتَ، ذَيْ مُتُ عَثِكِنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Amma idan adali ya bar yin adalci, ya aikata mugunta, ya yi abubuwa masu banƙyama waɗanda mugu yake aikatawa, zai rayu? Ayyukansa na adalci waɗanda ya aikata, ba za a tuna da su ba, faufau. Zai mutu saboda rashin amincin da ya yi da laifin da ya aikata.