Ezekiel 19:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma aka tumɓuke ta cikin fushi aka jefar da ita a ƙasa. Iskar gabas ta sa ta yanƙwane, aka kakkaɓe ’ya’yanta; rassanta masu ƙarfi suka bushe wuta kuma ta cinye su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا عَكَ تُمْٻُكٜىٰ إِتَاثٜىٰنَّنْ دَ ڢُشِے، عَكَ جٜىٰڢَرْ دَشِ حَرْ ڧَسَا؞ إِسْكَرْ غَبَسْ تَبُوسَرْ دَشِ، یَیَنْسَ كُمَ عَكَ كَكَّٻٜىٰ؞ رَسَّنَّنْ مَاسُ ڧَرْڢِے سُنْ بُوشٜىٰ، وُتَا كُمَ تَثِنْيٜىٰسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma aka tumɓuke kurangar inabin da fushi, Aka jefar da ita ƙasa. Iskar gabas ta busar da ita, 'Ya'yanta suka kakkaɓe, Rassanta masu ƙarfi sun bushe, wuta kuwa ta cinye su.