Ezekiel 19:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wuta ta fito daga jikin rassanta ta cinye ’ya’yanta. Babu sauran reshe mai ƙarfin da ya rage a kanta da ya dace da sandar mai mulki.’ Wannan waƙa ce kuma za a yi amfani da ita a matsayin makoki.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وُتَا تَڢِتُواْ دَغَ جِكِنْسَ تَثِ رَسَّنْسَ حَرْ ذُوَا یَیَنْسَ؞ يَنْذُ بَذَاعَ سَامِ رٜىٰشٜىٰ مَيْ ڧَرْڢِبَ، بَا وَنِ رٜىٰشٜىٰ، كُواْ طَيَ، وَنْدَ يَثَنْثَنْثِ يِنْ سَنْدَنْ مُلْكِ؞› «وَنَّنْ وَاڧَرْ مَكُواْكِثٜىٰ، أَنَ أَمْڢَانِ دَ عِتَ مَكُواْكِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wuta ta fito daga jikinta Ta cinye rassanta da 'ya'yanta, Don haka ba wani reshe mai ƙarfi da ya ragu, wanda zai zama sandan mulki. Wannan makoki ne, ya kuwa tabbata makoki.’ ”