Ezekiel 20:27 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Saboda haka, ɗan mutum, ka yi magana da mutanen Isra’ila ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a wannan kuma kakanninku suka saɓe ni ta wurin yashe ni.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«سَبُواْدَ حَكَ، يَا كَيْ طَنْ مُتُمْ، سَيْ كَيِمَغَنَ دَ غِدَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ، كَثٜىٰ، ‹إِنْجِنِ عُبَنْغِجِ يَهْوٜىٰهْ ، حَكَمَا كَاكَنِّنْكُ سُكَ سَٻَ مِنِ تَوُرِنْ ڧِنْ أَمِنْثٜىٰوَ دَنِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Domin haka, ya ɗan mutum, ka yi magana da mutanen Isra'ila ka ce, ‘Ni Ubangiji Allah, na ce kakanninku sun saɓe ni da ba su amince da ni ba.