Ezekiel 20:30 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Domin haka ka faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa za ku ƙazantar da kanku yadda kakanninku suka yi ne ku yi sha’awar mugayen siffofinsu?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«سَبُواْدَ حَكَ كَثٜىٰ وَغِدَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ، ‹إِنْجِنِ عُبَنْغِجِ يَهْوٜىٰهْ ، كُواْ ذَاكُ ڧَظَنْتَرْدَ كَنْكُ كَمَرْ يَدَّ كَاكَنِّنْكُ سُكَيِ؟ ذَاكُبِے أَبُبُوَنْ ڧَظَنْتَا وَطَنْدَ سُكَيِ؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Domin haka ka ce wa mutanen Isra'ila, ‘Ni Ubangiji Allah na ce za ku ƙazantar da kanku kamar yadda kakanninku suka yi? Za ku bi abubuwan da suka yi na banƙyama?