Ezekiel 20:40 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gama a kan dutsena mai tsarki, dutse mai tsayi na Isra’ila, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, a can a ƙasar gidan Isra’ila gaba ɗaya za su bauta mini, a can kuwa zan karɓe su. A can zan bukaci hadayunku da sadake sadakenku mafi kyau, tare da dukan tsarkakan hadayunku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
« ‹غَمَا إِنْجِنِ عُبَنْ‌غِجِ يَهْوٜىٰهْ ، عَكَنْ تُدُنَ مَيْ ڟَرْكِے كَطَيْ ذَاكُ بَوْتَا مِنِ؞ عَثَنْ كَنْ تُدُ مَيْ ڟَيِ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ، عَثَنْ ڧَسَرْ نٜىٰ دُكَنْ غِدَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ ذَاسُ بَوْتَا مِنِ؞ عَثَنْ نٜىٰ ذَنْ كَرْٻٜىٰسُ، عَثَنْ نٜىٰ كُمَ ذَنْ نٜىٰمِ بَيٜىٰ بَيٜىٰنْكُ دَ ݣَوْتَنْكُ مَڢِے ݣَوْ، تَرٜىٰدَ دُكَنْ هَدَايُنْكُ مَاسُ ڟَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Gama a kan dutsena ne mai tsarki, wato a bisa ƙwanƙolin dutsen Isra'ila, dukan mutanen Isra'ila za su bauta mini a ƙasar, a nan ne zan karɓe su. A nan kuma zan nemi sadake-sada-kenku, da hadayunku mafi kyau.