Ezekiel 21:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Saboda haka fa, ɗan mutum ka yi annabci ka kuma tafa hannuwanka. Bari takobi ya yi sara sau biyu, har sau uku ma. Takobin kisa ne, takobi ne don kisa mai girma, zai kewaye su a kowane gefe.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«كَيْ كُمَ، يَا كَيْ طَنْ مُتُمْ، كَيِ أَنَّبْثِ، كَبُغَ حَنُّوَنْكَ؞ كَكَطَ تَكُواْبِے سَوْ بِيُ، حَرْ مَا سَوْ عُكُ، تَكُواْبِے نٜىٰ دُواْمِنْ كِسَا؞ تَكُواْبِے نٜىٰ نَكَشٜىٰ كَشٜىٰ دَيَوَ، كُمَ يَنَ كٜىٰوَيٜىٰ دَسُو؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Domin haka, ya kai ɗan mutum, ka yi annabci, ka tafa hannuwanka, ka kaɗa takobi sau biyu, har sau uku. Takobin zai kashe waɗanda za a kashe. Takobi ne na yin kashe-kashe mai yawa. Zai kewaye su.