Ezekiel 21:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Domin zukata su narke da yawa kuma su fāɗi, na tsai da takobin kisa a dukan ƙofofinsu. Kash! A sa ya haska kamar walƙiya, ana riƙe da shi don kisa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تَكُواْبِنْ ذَيْسَا ذُوثِيَارْسُ سُنَرْكٜىٰ، دَ ڟُواْرُواْ دَيَوَ كُمَ ذَاسُيِ تَڢَاطُوَ؞ عَبَاكِنْ دُكَنْ ڧُواْڢُواْڢِنْسُ نَكَكَّڢَ تَكُواْبِے؞ أَهَ! أَنْيِشِ دُواْمِنْ يَيِ وَلْڧِيَ، أَنْوَاسَ شِ دُواْمِنْ كَشٜىٰ كَشٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zai sa zukatansu su narke, da yawa kuma su fāɗi a ƙofofinsu. Na ba da takobi mai walƙiya. An yi shi kamar walƙiya, an wasa shi don kashe-kashe.