Ezekiel 23:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Za su yi gāba da ke da kayan yaƙi, kekunan yaƙi da kekunan doki da mutane masu yawa; za su ja dāgā a kanki a kowane gefe da garkuwoyi manya da ƙanana da kuma hulunan kwano. Zan miƙa ke gare su don hukunci, za su kuma hukunta ki bisa ga shari’arsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاسُ ذُواْ دَغَ أَرٜىٰوَ سُڢَاطَ مِكِ دَ يَاڧِ دَ ڧُنْغِيَرْ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِنْ يَاڧِ دَ كٜىٰكُنَنْ شَانُو دَ ضُنْدُنَارْ سُواْجُواْجِ؞ ذَاسُ كَڢَ مِكِ سَنْسَنِنْ يَاڧِ عَكُواْوَنٜىٰ غٜىٰڢٜىٰ دَ ڧأَنَانً غَرْكُوَ دَ مَنْيَنْ غَرْكُوَ دَ هُولَرْ ݣُونُواْ؞ ذَنْبَاسُ إِيكُواْ سُيِ مِكِ حُكُنْثِ، سُكُوَ حُكُنْتَكِ بِسَغَ يَدَّ سُكَغَ دَامَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za su zo daga arewa su yi yaƙi da ke da karusai, da kekunan dawakai, da rundunar mutane. Za su kafa miki sansani a kowace sashi su yi yaƙi da ke da sulke, da garkuwa, da kwalkwali. Zan danƙa shari'a a hannunsu, za su kuwa shara'anta ki da irin shari'arsu.