Ezekiel 23:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sunan babbar Ohola, ƙanuwarta kuwa Oholiba. Sun zama nawa suka kuma haifi ’ya’ya maza da mata. Ohola ita ce Samariya, Oholiba kuwa ita ce Urushalima.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عُواْهُواْلَ عِتَثٜىٰ بَبَّ، عُواْهُواْلِبَ عِتَثٜىٰ ڧَرَمَ؞ سُنْ ذَمَ نَوَ، سُنْ كُوَ حَيْڢِ یَیَ مَظَا دَ مَاتَا؞ غَمٜىٰ دَ سُونَيٜىٰنْسُ كُوَ، عُواْهُواْلَ عِتَثٜىٰ سَمَرِيَ، عُواْهُواْلِبَ عِتَثٜىٰ عُرُوشَلِيمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sunan babbar Ohola, sunan ƙanwar kuwa Oholiba. Sun zama nawa, sun haifi 'ya'ya mata da maza. A kan sunayensu kuwa Ohola ita ce Samariya, Oholiba kuwa ita ce Urushalima.