Ezekiel 25:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan yi musu babbar sakayya da hukunci mai tsanani cikin hasalata. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na ɗauki fansa a kansu.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَنْيِ مُسُ بَبَّرْ رَامُوَا دَ حُكُنْثِ مَيْ ڟَنَنِ؞ سَعَدَّ نَيِ وَنَّنْ رَامُوَا عَكَنْسُ، ذَاسُ سَنِ ثٜىٰوَ نِنٜىٰ يَهْوٜىٰهْ ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zan yi musu babbar sakayya da hukunci mai tsanani. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na ɗauki fansa a kansu.”