Ezekiel 25:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
saboda haka zan miƙa hannuna gāba da ku in kuma ba da ku ganima ga al’ummai. Zan datse ku daga al’ummai in kuma kore ku daga ƙasashe. Zan hallaka ku, za ku kuwa san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تُواْ، غَاشِ، نَا مِيڧَ هَنُّونَ مَيْ إِيكُواْ نَغَابَادَكُو؞ ذَنْ بَاشٜىٰكُ أَ حَنُّنْ أَلْعُمَّيْ، كُذَمَ كَمَرْ كَايَنْ دَ عَكَ ݣُوشٜىٰ عَيَاڧِ؞ ذَنْ كَوَرْ دَكُو دَغَ ڧَبِيلُ، ذَنْسَا أَ هَلَّكَ ڧَسَرْكُ أَ شَارٜىٰ سُونَنْكُ دَغَ ثِكِنْ ڧَبِيلُ؞ ذَاكُ كُوَ سَنِ ثٜىٰوَ نِنٜىٰ يَهْوٜىٰهْ ؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
domin haka zan miƙa hannuna gāba da ku, zan bashe ku, ku lalace a ƙasashe, zan hallaka ku. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji.”