Ezekiel 26:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wa Taya. Ƙasashen da suke a bakin teku ba za su girgiza saboda ƙarar fāɗuwarki, sa’ad da nishin waɗanda aka yi wa rauni da kashe-kashen da aka yi a cikinki suka faru ba?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«إِنْجِنِ عُبَنْ‌غِجِ يَهْوٜىٰهْ ، غَ أَبِنْ نَكٜىٰ ڢَطِ عَكَنْ تَيَ؞ يَنْكُنَنْ بَاكِنْ تٜىٰكُنْكِ ذَاسُ غِرْغِظَ يَايِنْ دَ سُكَجِ ڧَارَرْ ڢَاطُوَرْكِ دَ نِيشِنْ وَطَنْدَ عَكَيِ مُسُ رَوْنِ دَ إِيهٌ كَشٜىٰ كَشٜىٰنْ دَ عَكَيِ عَثِكِنْكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji Allah ya ce wa Taya, “Sa'ad da kika fāɗi, ƙasashen da suke a gāɓar teku za su girgiza saboda amon fāɗuwarki, da nishin waɗanda ake yi wa rauni, da kashe-kashen da aka yi a cikinki.