Ezekiel 26:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan za su yi makoki game da ke su ce, “ ‘Yaya kika hallaka haka nan, ya birnin da ta yi suna, cike da mutanen teku! Ke da kika zama mai ƙarfi cikin tekuna, ke da mazauna cikinki; kin sa tsoronki a kan dukan waɗanda suka zauna a can.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاسُيِ مَكُواْكِ دُواْمِنْكِ سُثٜىٰ، « ‹يَيَ عَكَيِ كِنْ ٻَثٜىٰ دَغَ بَاكِنْ تٜىٰكُ، كٜىٰ دَ كِكٜىٰ سَنَنّٜىٰنْ بِرْنِ؟ يَيَ عَكَيِ كِنْ ٻَثٜىٰ دَغَ بَاكِنْ تٜىٰكُ، كٜىٰ دَ كِكَ تَٻَ ذَمَ ڟِبِرِے مَيْ ڧَرْڢِے عَتٜىٰكُ، كٜىٰ دَ مَذَوْنَنْكِ سُنْ تَٻَ ذَمَ أَبِنْ ڟُواْرُواْ غَ دُكَنْ وَطَنْدَ سُكٜىٰ ذَمَ كٜىٰوَيٜىٰ دَكٜىٰ؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za su yi makoki saboda ke, su ce, ‘Ke wadda ake zaune cikinki, kin bace daga tekuna, Ya shahararren birni, wanda yake babba a bakin teku, Ke da mazaunan da suke cikinki, kun sa mazaunan gāɓar teku su ji tsoro!