Ezekiel 27:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Mutanen Farisa, Lidiya da Fut su ne suka zama sojoji a cikin mayaƙanki. Sun rataye garkuwoyinsu da hulunan kwano a katangarki, suna kawo miki daraja.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ ڢَٰشِيَ دَ نَ لُدْ دَ نَ ڢُتْ، سُواْجُواْجِنْكِ نٜىٰ مَاسُ عِيَ يَاڧِ، مَاسُ رَاتَيَ غَرْكُوُاْيِ دَ هُولَرْ يَاڧِ عَثِكِنْكِ، مَاسُ سَامُواْ مِكِ طَوْكَكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“ ‘Mutanen Farisa, da na Lud, da na Fut suna cikin sojojinki don su yi miki yaƙi. Sun rataya garkuwoyi, da kwalkwali a cikinki. Sun samo miki daraja.