Ezekiel 27:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Mutanen Damaskus sun ga abin da za ki iya bayarwa sai suka yi ciniki da ke, ta sayi kayanki da ruwan inabi daga Helbon, da ulu daga Zahar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ دِمَشْڧُ سُنْيِ كَاسُوَنْثِ دَكٜىٰ سَبُواْدَ يَوَنْ كَايَنْ كَاسُوَنْثِنْكِ دَ يَوَنْ أَرْزِڧِنْكِ نَعَبُبُوَ إِرِ إِرِ؞ سُنْ سَيَرْ دَ ضُوً إِنَبِے نَ هٜىٰلْبُوانْ دَ نَڢَضٍ عُلُ دُواْمِنْ سَامُنْ كَايَنْكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dimashƙu kuma ta zama abokiyar cinikinki saboda yawan kayan cinikinki da yawan dukiyarki. Ta sayi kayanki da ruwan inabin Helbon, da farin ulu.