Ezekiel 27:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘’Yan kasuwan Sheba da Ra’ama sun yi ciniki da ke; suka sayi kayanki da kayan yaji mafi kyau iri-iri, da duwatsu masu daraja iri-iri, da zinariya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
یَنْ كَاسُوَنْثِ دَغَ شٜىٰبَ دَ رَعَمَ سُكَيِ كَاسُوَنْثِ دَكٜىٰ؞ سُكَ سَيَرْ دَ كَايَنْ يَجِ مَڢِے ݣَوْ دَ دُوَڟُو مَاسُ دَرَجَ إِرِ إِرِ دَ ظِينَارِيَ دُواْمِنْ سَامُنْ كَايَنْكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
'Yan kasuwar Sheba da Ra'ama sun sayi kayanki da kayan yaji mafi kyau iri iri, da duwatsu masu daraja iri iri, da zinariya.