Ezekiel 28:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ɗan mutum, ka faɗa wa mai mulkin Taya cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Cikin alfarmar zuciyarka ka ce, “Ni allah ne; ina zama a kan kursiyin allah a tsakiyar tekuna.” Amma kai mutum ne ba allah ba, ko da yake ka ɗauka kana da hikima kamar allah.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«يَا كَيْ طَنْ مُتُمْ، كَڢَطَا وَ سَرْكِنْ تَيَ، كَثٜىٰ، « ‹إِنْجِنِ عُبَنْغِجِ يَهْوٜىٰهْ ، يَا سَرْكِنْ تَيَ، كَيِ غِرْمَنْ كَيْ حَرْ كَثٜىٰ، «نِے وَنِ اللَّهْ نٜىٰ، إِنَ كُمَ ظَوْنٜىٰ عَكَنْ كُجٜىٰرَرْ مُلْكِ؞ كَمَرْ وَنِ اللَّهْ، نَكٜىٰ ظَوْنٜىٰ أَڟَكِيَرْ تٜىٰكُ؞» عَمَّا دُكْدَهَكَ، كَيْ مُتُمْ نٜىٰ كَوَيْ، بَوَنِ اللَّهْ بَ، كُواْدَيَكٜىٰ كَطَوْكِ كَنْكَ كَيْ مَيْ حِكِمَ نٜىٰ كَمَرْ اللَّهْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Dan mutum, ka faɗa wa Sarkin Taya, cewa Ubangiji Allah ya ce, ‘Da yake zuciyarka ta cika da alfarma, Har ka ce kai allah ne, Kana zaune a mazaunin allah, kana zaune a tsakiyar tekuna, To, kai mutum ne kawai, ba allah ba, Ko da yake ka aza kanka mai hikima ne kamar Allah.