Ezekiel 28:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan aika da annoba a kanta in kuma sa jini ya zuba a titunanta. Kisassu za su fāɗi a cikinta, da takobi yana gāba da ita a kowane gefe. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَنْ عَيْكَ دَ بَلَعِ عَثِكِنْكِ، دَ جِنِ عَتِيتُنَنْكِ؞ وَطَنْدَ تَكُواْبِے يَثِسُ، ذَاسُ ڢَاطِ أَڟَكِيَرْكِ، تَكُواْبِے ذَيْ يِغَابَادَكٜىٰ عَتَكُواْوَنٜىٰ غٜىٰڢٜىٰ؞ سَعَنً ذَاسُ سَنِ ثٜىٰوَ نِنٜىٰ يَهْوٜىٰهْ ؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zan aukar mata da annoba da jini a titunanta. Waɗanda za a ji musu rauni da takobi Za su fāɗi matattu a tsakiyarta. Za a tasar mata a kowane waje. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.’ ”