Ezekiel 29:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yi masa magana ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Ina gāba da kai, Fir’auna sarkin Masar, kai babban mugun dodon ruwa kwance cikin rafuffukanka. Ka ce, “Nilu nawa ne; na yi shi wa kaina.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَثٜىٰ، « ‹إِنْجِنِ عُبَنْ‌غِجِ يَهْوٜىٰهْ ، إِنَ غَابَادَكَيْ سَرْكِے ڢِرْعَوْنَ نَ مَصَرْ، كَيْ مُوغُنْ دُواْدُواْ مَيْ صِڢَّرْ مَثِيجِنَّنْ، مَيْ ݣُونْثِيَ أَڟَكِيَرْ حَنْيَرْ ضُوَيٜىٰ، كَنَ ثٜىٰوَ «أَيْ، كُواْغِنْ نِلُ نَوَنٜىٰ، نِے نَا يِشِ دُواْمِنْ كَيْنَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ka yi magana, ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Ga shi, ina gāba da kai, kai Fir'auna Sarkin Masar, Babban mugun dabba wanda yake kwance a tsakiyar koguna, Wanda yake cewa, Kogin Nilu naka ne, kai ka yi shi.