Ezekiel 3:20 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Har yanzu, in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya aikata mugunta, na kuma sa abin tuntuɓe a gabansa, zai mutu. Da yake ba ka yi masa kashedi ba, zai mutu saboda zunubinsa. Ba za a tuna da abin adalcin da ya yi ba, zan kuwa nemi hakkin jininsa a hannunka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«عِدَنْ كُمَ مَيْ أَدَلْثِے يَجُويَ دَغَ أَدَلْثِنْسَ يَكُمَ عَيْكَتَ رَشِنْ غَسْكِيَ، نِے كُوَ نَا سَا أَبِنْ سَا تُنْتُٻٜىٰ أَغَبَنْسَ، ذَيْ مُتُ؞ ذَيْ مُتُ سَبُواْدَ ذُنُوبِنْسَ؞ أَيُّكَنْ أَدَلْثِنْ دَ يَيِ، بَذَاعَ تُنَ بَ، عَمَّا سَبُواْدَ بَكَجَا مَسَ كُنّٜىٰ بَ، ذَنْ نٜىٰمِ أَلْحَكِنْ جِنِنْسَ دَغَ حَنُّنْكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Idan kuma adali ya bar adalci sa'an nan ya aikata zunubi, ni kuwa na sa abin tuntuɓe a gabansa, zai mutu. Zai mutu saboda zunubinsa domin ba ka faɗakar da shi ba. Ba za a tuna da ayyukansa na adalci waɗanda ya yi ba, amma zan nemi hakkin jininsa a hannunka.