Ezekiel 3:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Hannun Ubangiji ya kasance a kaina a can, ya kuma ce mini, “Tashi ka fita zuwa fili, a can kuwa zan yi maka magana.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَانً سَيْ إِيكُوانْ حَنُّنْ يَهْوٜىٰهْ يَذُواْ عَكَيْنَ أَوُرِنْ، يَكُوَثٜىٰ مِنِ «تَاشِ، كَتَڢِے ثِكِنْ ݣُورِ، ثَنْ ڢَا ذَنْيِ مَغَنَ دَكَيْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ikon Ubangiji yana tare da ni, Ubangiji kuwa ya ce mini, “Tashi, ka tafi ka tsaya a fili, a can zan yi magana da kai.”