Ezekiel 3:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka na tashi da tafi fili. Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta tsaya a can, kamar ɗaukakar da na gani kusa da Kogin Kebar, sai na fāɗi rubda ciki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ نَتَاشِ نَتَڢِے ݣُورِنْ، سَيْغَا ڧُنْشِنْ حَصْكٜىٰنْ طَوْكَكَرْ يَهْوٜىٰهْ يأَنَانً ڟَيٜىٰ أَوُرِنْ، كَمَرْ ڧُنْشِنْ حَصْكٜىٰنْ طَوْكَكَرْدَ نَغَنِ أَدَا عَبَاكِنْ كُواْغِنْ كٜىٰبَرْ؞ سَيْنَڢَاطِ دَ ڢُسْكَتَ حَرْ ڧَسَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai na tashi na tafi na tsaya a fili, sai ga ɗaukakar Ubangiji a wurin, a tsaye kamar ɗaukakar da na gani a bakin kogin Kebar. Sai na fāɗi rubda ciki.