Ezekiel 3:27 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma sa’ad da na yi maka magana, zan buɗe bakinka za ka kuwa faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.’ Duk mai ji ya ji, kuma duk wanda ya ƙi ji, ya ƙi ji; gama su gida ne na ’yan tawaye.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا سَعَدَّ نَيِ مَغَنَ دَكَيْ، ذَنْ بُوطٜىٰ بَاكِنْكَ، ذَاكَثٜىٰ مُسُ، ‹إِنْجِنِ عُبَنْ‌غِجِ يَهْوٜىٰهْ ؞› بَرِ وَنْدَ ذَيْجِے، يَجِ، بَرِ كُمَ وَنْدَ ذَيْڧِے، يَڧِ، غَمَا سُو یَنْ تَاوَيٜىٰنٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma sa'ad da na yi magana da kai, zan buɗe bakinka, kai kuwa za ka yi musu magana, ka ce, ‘Ubangiji ya ce, wanda zai ji, to, ya ji, wanda kuma zai ƙi ji, ya ƙi ji,’ gama su 'yan tawaye ne.”