Ezekiel 30:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shi da sojojinsa, mafi bantsoro cikin al’ummai, za a kawo don su hallaka ƙasar. Za su zāre takuba a kan Masar su kuma cika ƙasar da kisassu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
شِ دَ سُواْجُواْجِنْ أَلْعُمَّرْسَ، أَلْعُمَّ مَرَرْ تَوْسَيِ ڢِيٜىٰدَ سَوْرَنْ أَلْعُمَّيْ، ذَاعَ كَٰوُاْسُ دُواْمِنْ سُهَلَّكَرْ دَ ڧَسَرْ؞ ذَاسُ ذَارٜىٰ تَكُواْبِنْسُ عَكَنْ مَصَرْ، سُثِكَ ڧَسَرْدَ غَوَوَّكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Shi da mutanensa, Mutane mafi bantsoro a cikin sauran al'umma, Za a kawo su don su hallakar da ƙasar. Za su zare takubansu a kan Masar, Su cika ƙasar da gawawwaki.