Ezekiel 30:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan kafe rafuffukan Nilu in sayar da ƙasar ga mugayen mutane; ta hannun baƙi zan sa ƙasar ta lalace da kome da yake cikinta. Ni Ubangiji na faɗa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَنْسَا كُواْغِنْ نِلُ يَبُوشٜىٰ، إِنْ سَيَرْ دَ ڧَسَرْ أَ حَنُّنْ مُوغَيٜىٰنْ مُتَنٜىٰ؞ ذَنْ كَٰوُاْ هَلَّكَرْوَ عَكَنْ ڧَسَرْ دَ كُمَ عَكَنْ دُكْ أَبِنْدَ يَكٜىٰ عَثِكِنْتَ تَهَنُّنْ بَاڧِ؞ نِے عُبَنْ‌غِجِ يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zan busar da Kogin Nilu, Zan kuma sayar da ƙasar ga mugaye. Zan sa ƙasar ta lalace Da dukan abin da yake cikinta, Ta hannun baƙi, Ni Ubangiji, na faɗa.”